Jihar Arewa ta Gabas

Jihar Arewa-maso-Gabas tsohuwar yanki ce ta mulki a Najeriya. An ƙirƙire ta ne a ranar 27 ga watan Mayun 1967 daga sassan Yankunan Arewa. Babban birnin Jihar a lokacin itace birnin Maiduguri. Yankin Arewa-maso-gabas ta shahara wajen noma da isasshen abinci. A ranar 3 ga watan Fabrairun 1976 aka raba jihar zuwa jihohin Bauchi, Borno da Gongola. Daga baya an cire jihar Gombe daga Jihar Bauchi, jihar Yobe daga Borno sannan yankin Gongola ta rabu zuwa jihar Taraba da Adamawa.


Developed by StudentB